1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar dokoki Pakistan ta yi tir da harin da Amirka ta kai na kisan Bin Laden

May 14, 2011

Pakistan za ta kuma gudanar da nazari mai zurfi game da haɗin kan ayyukan soji tsakaninta da Amirka.

Firaministan Pakistan Yusuf Raza Gilani lokacin jawabinsa ga 'yan majalisaHoto: picture-alliance/dpa

'Yan majalisar dokokin Pakistan sun amince da wani ƙuduri wanda yayi tir da matakan da Amirka ta ɗauka na harin da ta kai wanda ya halaka shugaban Al-Qaida, Osama Bin Laden da cewa ya saɓa wa 'yancinta na 'yantacciyar ƙasa. Ƙudurin ya kuma yi kira da kafa wani kwamitin bincike mai zaman kansa game da gazawar rundunar sojin Pakistan ɗin, da ta kasa gano maɓoyar Bin Laden. Pakistan dai na shan kakkausan suka daga Amirka saboda rashin yin wani kataɓus na yaƙi da masu tsattsauran ra'ayi. Amirka dai na gudanar da na ta binciken kan yadda Bin Laden ya samu maɓoya a Pakistan lokaci mai tsawo ba tare da an gano shi ba. A halin yanzu majalisar dokokin ta Pakistan ta ba da shawarar yin nazari mai zurfi ga haɗin aikin soji da tsakanin ƙasar da Amirka kana ya yi kira da a kawo ƙarshen hare-haren jirgin sama da bai da matuƙi da Amirka ke kaiwa akan masu tsattsauran ra'ayi a yankin kan iyaka da Afganistan.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Halima Balaraba Abbas