Afirka ta Kudu an sake zaben Cyril Ramsphosa
May 22, 2019Talla
Cyril Ramaphosa wanda aka sake zaba ba da wani mamaki ba, an shirya cikin kwanaki na gaba zai bayyana sunayen sabbin manbobin majalisar minitocin gwamnatinsa. Wace ke da jan aiki a gabanta na yaki da cin hanci a karbar rashawa tare da sake farfado da tattalin arzikin kasar ta Afirka ta Kudu da ke tafe tanga-tangal.