1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar dokokin EU ta cika shekaru 70

Usman Shehu Usman
November 22, 2022

Majalisar dokokin Kungiyar Tarayyar Turai ta EU wadda ke da wakilai 705 daga ta cika shekaru 70 da kafuwa.

EU Conference on the Future of Europe
'Yan majalisar Kungiyar EU yayin wani zama da suka yi a bayaHoto: Philippe Stirnweiss/European Union 2022

Ita dai wannan majalisar fara kafata ne a matsayin kungiyar tara kudin fito na karafa da kwal, biyo bayan barnar da yakin duniya na biyu ya haddasa a Turai. Yanzu haka dai majalisar na da mambobi 705 daga kasashe 27 na Kungiyar EU.

Tsarin aiki a majalisar dokokin EU na da sarkaki inji sabuwar 'yar majalisa Kira Peter HansenHoto: FREDERICK FLORIN/AFP

Charles Goerens dan kasar Luxembourg shi ne dan majalisar na farko da aka zaba kai tsaye. An haife shi a shekarar 1952, wanda a wannan lokacin ne aka kafa majalisar. A hirarsa da DW ya ce "komai ya ya zame min na daban don duk abubuwan sabbi ne yanzu kama daga tsarin aiki da dokoki da ma abokan aiki.

Ita kuwa Kira Peter Hansen daga kasar Denmark wadda ita ce 'yar majalisa mafi karanci shekaru ta ce irin yadda aikin majalisar yake na da daurin kai sosai. 'Yar majalisar mai shekaru 24 da haihuwa na yin wa'adinta na farko ne a majalisar.

'Yan majalisar EU kan tsaya kai da fata wajen kare hakki da muradun Turai inji Charles GoerensHoto: Annegret Hilse/REUTERS

Da dama dai na aza ayar tambaya kan ainihin aikin wannan majalisar dokokin ta EU. Wannan ne ma ya sanya Charles Goerens da ya fi kowa dadewa a majalisar ya yi tsokaci inda ya ce guda daga cikin aikinsu shi ne kwato hakkin nahiyar inda ya kara da cewa ''a matsayinmu na 'yan majalisa dole ne mu yi gwagwarmayar kwato mana hakkinmu, ba mu da wani hakki a baya, babu kuma wanda ya ba mu hakki, dole ne mu tashi tsaye domin bukatarsa." 

Daya daga cikin babbar nasara da majalisar Kungiyar ta EU ta samu shi ne kudi bai daya na kasashe mambobi wato euro. Amma a maganar yanzu babban abin da ke zama mahawara mai zafi da ta fi daukar hankalin 'yan majalisar shi ne batun kare mahalli, ko da yake batun yakin Ukraine shi ma ya kasance abin da ke jan hankalin 'yan majalisar.