Majalisar dokokin Faransa ta amince da kudirin auren jinsi daya
February 2, 2013Talla
Majalisar dokokin kasar Faransa ta amince da gaggarumin rinjaye da kudirin nan da aka yi ta yin taƙadama akanta ta auren jinsi daya wacce ta janyo jerin zanga zanga na kungiyoyin masu fafutuka.
Dokar wacce yan majalisun dokoki 249 su ka kada kuri'ar amincewa da ita yayin da wasu 97 su ka hau kujerar naƙi, ta ce ƙarara a mataki daya na kudirin, kan abin da ke da muhimanci doka ta amince da aruren mutane biyu masu jinsi daya ko kuma banban.
Kuri'ar jan ra'ayi ya nuna yadda dokar ke da goyon baya, wanda ake saran Shugaba Francois Hollande da gungun masu mara baya ga jam'iyya mai mulki ta gurguzu, za su tabbatar da wannan nasarar yayin amincewa da dokar ranar 12 ga wannan wata na Febrairu.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman