Majalisar dokokin Girka ta amince da shirin tsuke aljihun gwamnatin
November 8, 2012Talla
Majalisar dokokin ƙasar Girka ta amince da shirin tsuke bakin aljihun gwamnatin, a yayin da a yau aka shiga cikin kwanaki na biyu na zanga zangar da duban jama'ar ƙasar suke yi domin yin addawa da shirin.
Tsarin na gwamnatin na rage kuɗaɗen da gwamnatin ta ke kashe wa da biliyan 13 da rabi ,wanda ke buƙatar samu ta barakin majalisar gabannin samun tallafi na ƙungiyar Tarrayar Turai da asusu bada lamuni na duniya kimanin biliyan 31;ya samu amincewa a majalisar da ƙaramin rinjayen da ya zarta ƙuri'u 151.
Fra ministan girka Antomi Samaras ya sanar da cewar wannan abi ne da ya zama ruwan dare gama dunia ya ce dole sai an daure.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Mahamadou Awal Balarabe