Jamus za ta shiga yakar IS gaba gadi a Siriya
December 4, 2015Talla
'Yan majalisar dokoki a kasar Jamus a ranar Juma'an nan sun amince da shirin kasar kai tsaye a fafata da ita a ayyukan da suka shafi murkushe mayakan IS a Siriya, wannan dai na zama wani bangare na amsa kiran neman tallafin babbar kawar ga Faransa wacce harin ta'addancin da kungiyar ta IS ta kaddamar a birnin Paris ya yi sanadin halaka mutane da dama.
Ya zuwa yanzu dai kasar ta Jamus za ta tura jiragen yakin nan masu suna Tanado gami da dakarun soja 1,200 bayan da 'yan majalisa 445 suka amince da wannan bukata yayin da 146 suka nuna kin amincewarsu.
Wannan yunkuri na Jamus dai na zama mafi girma a kasashen waje wanda ke zuwa makwanni uku bayan da masu ikirarin na Jihadi suka halaka mutane 130 a farmakin da suka kai a birnin Paris.