Majalisar Jamus ta amince da shirin ceton Girka
July 17, 2015Majalisar dokokin kasar Jamus ta Bundestag da gagarumin rinjaye ta amince da shirin ceton tattalin arzikin kasar Girka, domin tabbatar da matakan da kasashen Turai na kare Girka. A wannan Jumma'a majalisar ta jefa kuri'ar amincewar, inda 'yan majalisa 439 suka amince sannan 119 suka nuna rashin amincewa, kana 'yan majalisa 40 suka yi rowar kuri'unsu. Tun farko Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bukaci 'yan majalisar su ba da goyon baya bisa sabon shirin ceton tattalin arzikin Girka.
Merkel kamar Firaminista Alexis Tsipras na Girka ta fuskanci tawaye daga mambobin jam'iyya mai mulki, amma duk da haka majalisar dokokin ta Jamus da ta kunshi gwamnatin hadaka ta amince da shirin da gagarumin rinjaye. Karkashin sabon shiri za a yi amfanin da kudade kimanin Euro milyan dubu-85, wajen ceton tattalin arzikin Girka, yayin da kasar za ta aiwatar da matakan tsuke bakin aljihu.