Majalisar dokokin Japan ta zabi Shinzo Abe a mukamin sabon Firaminista
September 26, 2006Talla
An zabi shugaban jam´iyar Liberal Democrat LDP dake jan ragamar mulki a Japan, Shinzo Abe a matsayin FM kasar na 90, don ya gaji tsohon FM Junichiro Koizumi. Abe mai shekaru 52 da haihuwa ya lashe zaben ne a kuri´ar da majalisar dokoki ta kada dazu-dazun nan don samar da sabon FM kasar. A cikin makon jiya Abe ya lashe zaben zaman shugaban jam´iyar LDP da gagarumin rinjaye. Mista Abe wanda shi ne FM kasar mafi karancin shekaru na haihuwa tun bayan yakin duniya na biyu, ya ce zai nemi goyon bayan majalisa don yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima. Daga cikin shirye shiryen da gwamnatinsa ta sa a gaba sun hada da yiwa tsarin ba da ilimin kasar gyaran fuska, karfafa huldodin diplomasiya sai daukar matakan ta da komadar tattalin arzikin kasa.