1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Majalisar dokokin Kamaru ta ce shugaba Biya ya jinkirta zabe

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
July 10, 2024

'Yan jam'iyyar shugaba Biya ta CPDM da ke da rinjaye a majalisar ne suka amince da wannan kuduri

Paul Biya
Paul BiyaHoto: Stephane Lemouton/abaca/picture alliance

Majalisar dokokin kasar Kamaru ta sahale wa shugaba Paul Biya ikon jinkirta gudanar da zaben majalisun kasar, har zuwa shekarar 2026, matakin da 'yan adawa suka yi zargin cewa yunkuri ne kawai na kara nesanta su da neman madafun ikon shugabancin kasar a zaben badi.

Karin bayani:Kamaru: Matsalar tserewar kwararru zuwa Turai

Mambobin jam'iyyar shugaba Biya ta Cameroon People's Democratic Movement da ke da rinjaye a majalisar ne suka amince da wannan kuduri, wanda ya nuna cewa yanzu haka dai za a gudanar da zaben majalisar dokokin kasar a cikin watan Maris din shekarar 2026.

Karin bayani:Paul Biya ya yi wa sojoji garanbawul

Yayin da kuma za a gudanar da zaben shugaban kasa a cikin shekarar 2025 mai kamawa.

A na sa bangaren jagoran jam'iyyar adawa ta Social Democratic Front SDF Joshua Osih, ya ce wannan ba wani abu ba ne face karan tsaye ga tsarin dimukuradiyya.