1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Majalisa ta amince da kasafin kudin 2022

Gazali Abdou Tasawa RGB
December 15, 2021

Majalisar dokokin jamhuriyar Nijar ta amince da sabon kasafin kudin kasar na shekarar 2022 bayan ta share watanni kusan uku tana nazarinsa.

Niger Niamey | Parlament
Hoto: Gazali A. Tassawa/DW

A Jamhuriyar Nijar, majalisar dokokin kasar ta kada kuri’ar amincewa da sabon kasafin kudin kasa na shekara ta 2022 wanda gwamnati ta gabatar a gabanta. Majalisar ta amince da kasafin kudin ne bayan da ta share watanni kusan uku tana nazarinsa. Sai dai bayan zazzafar muhawara 'yan majalisar dokokin na bangaren adawa sun yi watsi da kasafin suna masu cewa bai yi daidai da bukatun al’umma da sauran matsaloli da kasa take fama da su ba. 

Shugaban majalisar dokokin Nijar Alhaji Seini Omar a lokacin da yake tabbatar da amincewar da majalisar dokokin kasar ta yi wa sabon kasafin kudin kasar na shekara mai kamawa, wanda ya tashi kan kudi biliyan dubu biyu da dari tara da takwas da ‘yan ka na CFA. ‘Yan majalisar dokokin sun amice da kasafin da kuri’u 129 a yayin da 37 suka kada kuri’ar kin amicewa da shi.

Sai dai sabanin shekarun da suka gabata, 'yan majalisar dokoki na bangaren adawa ba su fice daga zauren majalisar ba a lokacin kada kuri’ar. Amma kuma illahirinsu sun yi watsi da sabon  kasafin kudin  da kuri’u 37, suna masu zargin cewa akwai fannoni da dama masu muhimmanci da ya kamata a zuba kudade masu yawa da amma gwamnatin ta yi kememe.

Karin kimanin kudi biliyan 77 da rabi ne aka samu kan sabon kasafin kudin na shekara ta 2022 idan aka kwatanta shi da na wannan shekara ta 2021. Sai dai gwamnatin ta Nijar na sa ran samun kaso 53 daga cikin dari na sama da biliyan dubu biyu da dari tara na kudin CFA da kasafin kudin shekarar mai kamawa ya kunsa daga ketare.