1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a zabi sabon shugaban majalisar Turai

Gazali Abdou Tasawa
July 3, 2019

'Yan majalisar dokokin Turai na gudanar a wannan Laraba da zaben sabon shugaban majalisar da zai maye gurbin Antonio Tajani na Italiya a wani sabon wa'adi na tsawon shekaru biyu da rabi. 

Frankreich Strasbourg Europa Parlament
Hoto: Imago Images/Xinhua

'Yan majalisar dokokin Turai na gudanar a wannan Laraba da zaben sabon shugaban majalisar da zai maye gurbin  shugaban na yanzu Antonio Tajani na jam'iyyar masu kyamar baki ta Italiya a wani sabon wa'adi na tsawon shekaru biyu da rabi. 

Sabbin 'Yan majalisar Turan wadanda aka kaddamar a jiya Talata a birnin Brussels za su zabi sabon shugaban nasu bayan da a jiya Talata shugabannin kasashen Turai 28 suka zabi Ursula von der Leyen ministar tsaron kasar Jamus a matsayin sabuwar shugabar hukumar gudanarwa ta Tarayyar Turan, mukamin da amma zai tabbata bayan samun amincewar majalisar dokokin Turan a kuri'ar da za ta kada a makonni biyu masu zuwa. 

A sauran manyan mukaman Turan dai an nada Christine Lagarde ta kasar Faransa a matsayin shugabar Babban Bankin Turai na ECB, a yayin da aka zabi Firaministan Beljiyam Charles Michel na Jam'iyyar Liberal  a matsayin shugaban majalisar ministocin Turan. Ana sa ran kuma zaben Josep Borrell na kasar Spain a matsayin babban jami'in kula da harakokin waje na kungiyar ta EU.