1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

EU ta bukaci a kawo karshen luguden wuta a Gaza

Binta Aliyu Zurmi
January 18, 2024

Zauren Majalisar Tarayyar Turai ya yi kira da a gagauta kawo karshen luguden wuta da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza, da ma bukatar kungiyar Hamas ta sako duka mutanen da take garkuwa da su.

Brüssel Europaparlament Plenarsaal
Hoto: Ute Grabowsky/photothek/IMAGO

Kudurin majalisar da kakausar murya ya soki matakin ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai hari a Isra'ila, kazalika da murya daya 'yan majalisun sun ki amincewa da matakin ramuwar gayya da Isra'ila ta dauka wanda suka ce bai kai girman laifin da aka yi mata ba.

Yan majalisun dai sun kara da cewar Isra'ila na da yancin kare kanta, amma kuma ta yi shi daidai da dokokin kasa da kasa.

Sun bukaci duka bangarorin biyu da su gagauta mayar da wukaken su kube, domin kawo karshen kisan fararen hula da yanzu haka ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce adadinsu ya haura 24,000, sama da kwanaki dari da kaddamar da yakin.

 

Karin bayani: Yakin da Isra'ila ke gwabzawa da Hamas ya cika kwanaki 100