Majalisar Girka ta amince da kuri'ar raba gardama
June 28, 2015Talla
Majalisar dokokin kasar Girka ta amince da kada kuri'ar raba gardama kan amincewa ko watsi da shirin ceto tattalin arzikin kasar karkashin yarjejeniyar Tarayyar Turai da hukumar ba da lamuni ta duniya, IMF. 'Yan majalisa 179 daga cikin 300 suka kada kuri'ar amince a yi zaben na raba gardama ranar Lahadi mai zuwa 5 ga watan gobe na Yuli, kamar yadda Firaministan kasar Alex Tsipras ta bukata.
Sai dai bisa tsarin ceto tattali arzikin kasar ta Girka tilas zuwa ranar Talata kasar ta biya wani bangaren bashi hukumar IMF, abin da zai yi wuya idan ba a fadada tallafa wa tattalin arzikin kasar ta Girka ba.