Majalisar Italiya ta sallami Berlusconi
November 27, 2013Talla
Bayan da kotu ta same shi da laifin yin rufa-rufa kan kuɗin haraji, majalisar dattawan ƙasar Italiya ta kori Silvio Berlusconi, tsohon Firaministan ƙasar daga zaurenta. Shugaban majalisa ne da kansa ya faɗawa Berlusconi cewa, daga yanzu ba shi da kujera a majalisar, abinda ke nufin an salla me shi kenan.
Magoya bayan jam'iyar Berlusconi da ke cikin majalisar dai sun yi iya ƙoƙarinsu na hana wannan korar-kare da aka yi wa fitaccen dan siyasa kana hamshaƙin mai kuɗi a ƙasar Italiya. A watan Augusta kotu ta ɗaure Silvio Berlusconi na tsawon shekaru huɗu a gidan yari, bayan da aka same shi da laifin yin coge wajen biyan kuɗin harajin wani kamfaninsa na yaɗa labarai.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe