1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Jamus ta amince ceton tattalin arzikin Girka

Suleiman BabayoAugust 19, 2015

Majalisar dokokin Jamus da gagarumin rinjaye ta amince da shirin ceto tattalin arzikin kasar Girka mataki na uku cikin shekaru biyar

Deutschland Bundestag entscheidet über neue Griechenland-Hilfen
Hoto: Getty Images/A. Berry

A karo na biyu ke nan 'yan majalisar dokokin ke katse hutun lokacin bazara domin kada kuri'a kan matakin ceton tattalin arzikin kasar Girka, kuma galibin 'yan majalisar dokokin ta Bundestag sun amince da shirin bai wa kasar ta Girka kimanin kudaden da suka kai Euro milyan dubu-86.

Jim kadan bayan kammala jefa kuri'ar shugaban majalisar dokokkin ta Jamus Norbert Lammert ya tabbatar da sakomakon inda aka kada kuri'a 585 baki daya. 454 sun amince, yayin da 113 suka kada kuri'ar rashin amincewa, sannan 18 suka yi rowar kuri'unsu. Saboda haka wannan shiri ya samu karbuwa.

Sakamakon wannan mataki na majalisar dokokin kasar ta Jamus, ya tabbatar da cewa kasar za ta shiga cikin shirin ceton tattalin arzikin kasar ta Girka na shekaru biyar masu zuwa. Sai dai tuni Wolfgang Schaeuble ministan kudin kasar ta Jamus, wanda tun farko ya nemi majalisar da Busdestag ta kada kuri'ar amincewa da shirin, ya bayyana cewa kasar Girka ya dace ta dauki darasi sannan ta aiwatar da matakan da za su karfafa tattalin arzikin kasar.

Wolfgang Schaeuble ministan kudin JamusHoto: Getty Images/A. Berry

Wani abin da aka samu a majalisar ta Bundestag shi ne yadda wasu mambobin jam'iyyar CDU mai mulki ta Shugabar Gwamnati Angela Merkel suka juya baya wa shirin ceto tattalin arzikin, inda 'yan majalisa 63 suka yi wa shigabar gwamnatin tawaye. Tun farko wani jigo a cikin jam'iyyar ya yi gargadin cewa rashin mara baya ga shugabar gwamnatin Merkel ya zama tamkar cin amana.

Hoto: Reuters/A. Schmidt

Babbar jam'iyyar kawance a cikin gwamnatin ta SPD ta soki yadda jam'iyya mai ra'ayin sauyi ta gaza goyon bayan matakin, duk da cewa jam'iyyar Syriza mai mulkin Girka ta kasance mai ra'ayin sauyi. Thomas Oppermann ke zama jagoran jam'iyyar SPD a majalisar dokokin ta Bundestag.

Firamnista Alexis Tsipras na kasar Girka ya samu wata dama kan ceto shirin tattalin arzikin kasar da ke samun goyon bayan wadanda abun ya shafa.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani