1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Mata sun ce an yi rabon kura na mukamai

Gazali Abdou Tasawa AH
April 9, 2021

A Jamhuriyar Nijar kungiyoyin mata da dama na kasar sun koka dangane da abin da suka kira rabon kura da aka yi a cikin gwamnati inda aka ba su kujeru biyar kawai a sabuwar majalisar ministocin ta kasar.

Niger Niamey | Parlament
Hoto: Gazali A. Tassawa/DW

Daga cikin mambobi 33 da sabuwar majalisar ministocin gwamnatin firaminista Mahamadou Ouhoumoudou ta kunsa mata sun tashi ne da kujeru biyar wato uku daga jam’iyya mai mulki ta PNDS Tarayya da kuma daya  daya daga jam’iyyar MNSD NASARA da kuma ta MPR Jamhuriyar a yayin da sauran jam’iyyun suka kememe kasance maza sun yi kakagida. Tuni kuma wasu Kungiyoyin matan kasar ta Nijar suka soma nuna rashin jin dadinsu da wannan kasafi. To sai dai a daidai lokacin da wasu matan ke korafi da rabon kurar da suke zargin an yi masu a cikin sabuwar gwamnatin, wasunsu na ganin halin matan na son kai ne ya jawo musu wannan matsala. A bisa lisafin dokokin kasar ta Nijar dai ya kamata matan su samu kujeru tara zuwa goma a cikin sabuwar gwamnati a maimakon shida. Sai dai Hajiya Halima Sarmai mamba a kawancen kungiyoyin matan Nijar ta ce za su nemi gwamnatin ta sake lale. Ko ma dai mi ake ciki, tuni sabuwar gwamnatin ta kama aiki inda ta gudanar da taron majalisar ministocinta na farko a karkashin jagorancin sabon shugaban kasa Mohamed Bazoum.