1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Thailand ta amince da auren jinsi

Abdullahi Tanko Bala
June 18, 2024

Kungiyar LGBTQ ta yaba wa 'yan majalisar dokokin Thailand yayin da kasar zama kasa ta farko a nahiyar Asiya da ta amince da dokar auren Jinsi

Auren jinsi a Thailand
Hoto: Sakchai Lalit/AP/picture alliance

'Yan majalisar dokokin Thailand sun amince da dokar daidaita aure tsakanin jinsi inda ta kama hanyar zama kasa ta farko a kudancin Asia da ta amince da auren jinsi bayan kasashen Nepal da Taiwan wadanda su ma suka amince da auren jinsi.

Majalisar dattijan Thailand din ta amince da kudirin dokar wadda a yanzu za a gabatar wa Sarki Maha Vajiralongkorn domin amincewarsa.

Firaministan Thailand Srettha Thavisin, ya bayar da cikakken goyon baya ga al'ummar LGBTQ zai kuma karbi bakuncinsu a nan gaba domin shirya musu liyafa.