1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar tsaro ta yi zaman taro kan halin da Najeriya take ciki

July 31, 2014

A wani mataki na kokarin kawo karshen tashin hankalin dake zaman ruwan dare a arewacin Najeriya, majalisar magabatan kasar ta bada wa'adin watan Disamba da nufin kare ta'addancin dake kara ta'azaara a kasar.

Nigeria Armee Anschlag in Abuja 25.6.2014
Hoto: REUTERS

Sannu a hankali dai dan hakin da ka rena ya kama hanyar tsone ido cikin kasar, inda yanzu haka rikici na ta'addanci ya kama hanyar rikidewa ya zuwa na siyasa, da ma raba kan kasar dake fuskantar annobar yanzu, abun kuma da ya tilasa wani taron gaggawa a bangaren majalisar magabatan kasar da ta kamalla wani taron ta da yammaciyar yau a |Abuja sannan kuma tace ta ba kanta wa'adin watan Disamban dake tafe domin kawo karshen matsalar dake kara ta'azzara a halin yanzu.

Kauda banbanci da wariyar da ta kai har ga jihohi neman tabbatar da rijistar baki na waje ne dai ya tada hankula, tare da kafuwar wani kwamiti na wakilai shida da gwamnatin ta Abuja ta dorawa alhakin tabbatar da kawo karshen banbancin ta ko'ina. Majalisar da ke zaman mafi tasiri ga kasar dai tace tana shirin kara baki ga kasar da ko bayan matsalar ta ta'addancin ke kuma fuskantar barazanar rabuwa a tsakanin kudu da arewa sakamakon annobar dake sauyin launi da salo. Banbacin addini ne dai, a fadan gwamnan jihar Niger Babangida Aliyu, kuma daya a cikin yan kwamitin ke zaman ummul'abai'sin neman rushewar kasar, da ma kari na tada hankalin dake akwai a halin yanzu.

“Yadda muke abubuwa kullum kamar nuna banbanci ne, sai ace sai ka fadi inda ka fito, in kai an haife a Kano amma kuma kai mutumin Ogbomosho ne sai ace sai ka fadi inda ka fito. Da yardar Ubangiji dole ne mu koma, kuma mu yarda fa cewar ba wata PDP ko APC in ba Najeriya."

Fakewa a cikin rikici da nufin cika buri na siyasa, ko kuma tada hankali da suna na siyasar da,i majalisar ta kuma damu da karkatar da harin da aka kai ga madugu na adawar kasar a makon jiya, harin kuma da a fadar babban mashawarcin gwamnatin kasar akan tsaro Col Sambo Dasuki mai ritaya, ke da ruwa da tsaki da aiyyika na kungiyar Boko Haram zalla.

“ A cikin watan Fabrairu akwai inda Shekau ya fito yace su Janar Buhari kafirai ne, kuma za su gani, kuma suna bi. Saboda haka ace gwamnati ce tayi kuskure? Shi wannan sabon hari muna nazari, amma dai muna ganin kamar yara ne ake dauka a kautar musu da hankula, amma dai babu yan matan Chibok a ciki”

Madugun yan adawa a Najeriya, Janar Muhammad BuhariHoto: DW/N. Zango

Duk da cewar dai majalisar ta kamalla taron nata ba tare da aiyyana sabon babban Sufeton yan sandan kasar kamar yadda akai ta tsammanni tun farkon fari ba, kasancewar Suleman Abba tare da Sufeton dake shirin barin gado a fadar gwamnatin kasar da nufin ganawar sirri da shugaban kasar ya tabattar da hasashen nadin Abba dake zaman daya a cikin mukadassan Sufeton yan sandan na kasa.

Ko bayan yaki da ta'addancin da ya dora sunan kasar ta Najeriya bisa taswira maras kyau a duniya baki daya, babban kalubalen dake gaban sabon babban Sufeton dai na zaman taka muhimiyyar rawa wajen kaiwa ya zuwa tabbatar da zabukan dake iya karbuwa a tsakanin kowa.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Umaru Aliyu

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani