Majalisar Wakilan Amirka ta amince da rufe TikTok
March 14, 2024Talla
Majalisar Wakilan Amurka ta amince da kudurin da zai kai ga toshe shafin sada zumunta na Tiktok a kasar gaba daya. 'Yan majalisa 352 sun bai wa kamfanin mallakin kasar China watanni shida wa'adin ko dai ya sayar da TikTok ga Amurka ko kuma su toshe amfani da shi a kasar gaba daya.
Sai dai a yayin da kudurin hana TikTok din ya yi gaggawar wucewa a Majalsiar Wakilai, ana fargabar Majalsiar Dattawan kasar ka iya kin amincewa da yunkurin rufe TikTok din. To amma Fadar mulki ta White House ta ce Shugaba Joe Bidena shirye yake ya rattaba hannu a kan kudurin madamar majalisun kasra biyu suka amince da shi.