Majalisar wakilan Japan ta amince da komawar jiragenta na ruwa Afghanistan
January 11, 2008Talla
Majalisar wakilan ƙasar Japan ta jefa kuri’ar amincewa da sake komawar aiyukan sojojin ruwa na ƙasar don taimakawa aiyukan sojin Amurka da kawayenta a ƙasar Afghanistan. Jamiyar firaministan Yasuo Fakuda tayi anfani da rinjaye da take da shi a majalisar wakilan inda ta samu nasarar kan yan dawa da basa goyon bayan komawa Afghanistan. A watan Nuwamban bara ne rundunar sojin ruwa ta Japan ta kammala aiyukanta na bada mai ga jiragen sama da na ruwan Amurka da suke kan tekun Indiya kusa da Afghanistan,bayan da majalisar dattijan ƙasar ta ki amincewa da ƙara wa’adin aiyukan nasu. Jamian ƙasar sunce mai yiwuwa ne manyan jiragen ruwan Japan su koma Afghanistan cikin wata mai zuwa.