SiyasaIsra'ila
Majalisar Yahudawa ta bukaci goyon bayan Merz
September 18, 2025
Talla
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya halarci taron kungiyar a Frankfurt don bikin cikarta shekaru 75 da kafuwa.
An kafa majalisar kolin ta Yahudawa a Frankfurt shekaru biyar bayan kawo karshen yakin duniya na biyu.
Shugaban kungiyar Josef Schuster ya bukaci shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz da cewa kada ya kauce daga kudirinsa na goyon bayan Isra'ila ko da wasu kasashen Turai ko daidaikun 'yan majalisar dokoki za su nemi jan ra'ayinsa.
Tun dai bayan barkewar yakin Gaza Jamus ta kasance babbar mai goyon bayan kasar Israila.