Majalisar Yuganda ta fuskanci katsalandan
December 19, 2017Majalisar dokokin Yuganda ta dakatar da muhawarar da take gudanar a kan wa'adin shugabancin kasa bayan da wasu sojoji suka kutsa cikin zauren majalisar. Wata tashar talabijin ta wannan kasar da ke gabashin Afirka ta nuna hutunan 'yan majalisa da 'yan sanda da ke neman bayanai kan abin da ke faruwa. Sai dai rundunar sojojin Yugunda bata ce uffan game da aniyar sojojin ba.
Shugaba Yoweri Museveni ya nemi majalisar dokoki ta kwaskware dokar da ke hana duk dan kasar da ya zarta shekaru 75 da haihuwa tsayawa takara. Sai dai Museveni mai shekaru 73 da haihuwa a yanzu zai zarta wadannan shekaru kafin zaben 2021
Shi dai Museveni ya yi mulki Yuganda mai arzikin man fetur na tsawon shekara 31. Sai dai 'yan adawa da shugabannin addini suna hamayya da matakinsa na neman yin tazarce.