1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Makamai masu linzami daga Yemen sun fada Isra'ila

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
September 15, 2024

Tun cikin watan Nuwamban bara ne 'yan tawayen Houthi na Yemen suka fara kai hari Isra'ila da duk wasu jiragen ruwa masu alaka da ita da ke ratsawa ta baharmaliya

Hoto: Mohammed Huwais/AFP/Getty Images

Rundunar sojin Isra'ila ta ce makamai masu linzami da aka harba mata daga kasar Yemen a safiyar Lahadin nan, sun fada cikin tsakiyar kasar, to sai dai ba su jikkata kowa ba.

Karin bayani:Jiragen yakin Isra'ila sun yi barin wuta a Yemen

Sanarwar ta rundunar ta fitar ta ce makaman sun fada ne a wasu wuraren da babu kowa, sannan suka fashe, kuma suna nazartar yadda lamarin ya faru.

Karin bayani:Amurka ta kai hari kan tungar 'yan tawayen Houthi na Yemen

Tun a cikin watan Nuwamban bara ne 'yan tawayen Houthi na Yemen suka fara kai hare-hare kan Isra'ila da duk wasu jiragen ruwa masu alaka da ita da ke ratsawa ta baharmaliya, a wani mataki na nuna goyon baya ga Falasdinawa, sakamakon yakin da Isra'ila ke yi a Gaza.