1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Makashin mata a Kenya ya yi layar zana a ofishin 'yan sanda

August 20, 2024

'Yan sandan kasar Kenya sun bayyana cewar mutumin da ake zargin kashe wasu tarin mata tare da jefa gawarwakinsu cikin wani tafkin da ake zuba shara ya yi layar zana daga ofishinsu da ke birnin Nairobi.

Collins Jumaisi a lokacin da ake tuhumarsa da kisan mata 42 a gaban kotun Nairobi
Collins Jumaisi a lokacin da ake tuhumarsa da kisan mata 42 a gaban kotun NairobiHoto: Simon Maina/AFP

Mutumin mai suna Collins Jumaisi, ya tsere ne tare da wasu 'yan kasar Eritrea daga ofishin Gigiri, a cewar mai magana da yawun rundunar 'yan sandar Nairobi, Resila Onyango, inda ta ce an cafke Jumaisi a watan Yulin 2023, bayan samun sa da laifin kashe wasu mata shida tare da jefa gawarwakinsu cikin tafkin.

Karin bayani: An sake kama wani Pastor da kashe mabiyansa a Kenya 

'Yan sanda sun ce mutumin ya halaka mata kimanin 42 ciki har da matarsa, to amma lauyansa ya shaida wa kotu cewa an azabtar da mutumin domin ya amsa laifinsa, tare kuma da musanta zarge-zargen da ake masa.