Makomar Boko Haram bayan karbe Sambisa
December 29, 2016![Karikatur: Nigeria - Armee erobert Boko Haram Hochburg Sambisa](https://static.dw.com/image/36942754_800.webp)
Talla
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da cewar dakarun kasar sun karbe iko da babbar tungar 'yan Boko Haram da ke dajin Sambisa a jihar Borno, inda aka kame da dama a cikinsu. Tuni ma wasu mayakan Kungiyar Boko Haram suka mika wuya ga hukumomin Jihar Diffa ta Jamhuriyar Nijar.