1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar Gaddafi bayan an tsagaita wutar rikicin Libiya

July 20, 2011

Gwamnatin Faransa ta ce shugaban Libiya Muammar Gaddafi ka iya ci-gaba da zaman a ƙasarsa idan aka cimma shirin tsagaita wuta.

Hoto: AP

Ministan harkokin wajen Faransa Alain Juppe ya ƙasar Faransa na duba yiwuwar tabbatar wa shugaban Libiya Muammar Gaddafi 'yancin zama cikin ƙasarsa, idan ya amince ya wanke hannunsa daga dukkan harkoki na siyasa. Sai dai ministan harkokin wajen Libiya Abdelati el Obeidi ya faɗa a wata ziyara a birnin Mosko cewa Gaddafi ba zai sauka daga kan karagamr mulki ba. A kuma halin da ake ciki, a wata tattaunawa da suka yi a fadar Elysee ta birnin Paris, shugabannin 'yan tawayen Libiya sun yi kira ga shugaban Faransa Nikolas Sarkozy da ya ƙarfafa guiwar masu tayar da ƙayar bayan ta hanyar ba su ƙarin makamai, domin su ƙwace birnin Tripolis kuma su kifar da Gaddafi. A wani labarin kuma shugaban Afirka Ta Kudu Jacob Zuma da takwaransa na Tanzaniya Jakaya Kikwete sun nuna rashin jin daɗinsu ga yadda ake aiwatar da kudurin MDD kan Libiya, inji Bernard Membe ministan harkokin wajen Tanzaniya.

"Shugabannin biyu sun nuna matuƙar damuwa kan yadda ake aiwatar da ƙudurin saɓanin yarjejeniyar da aka cimma. Dukkan sassa ukun da ke rikicin wato dakarun NATO da na Libiya da kuma 'yan tawaye suna kashe mutane suna jefa rayukan 'yan Libiya cikin uƙuba. Wannan ba abin karɓuwa ba ne. Wannan shi ne matsayin AU."

A wannan Larabar tawagar shugaban Tanzaniya Jakaya Kikwete ta kammala ziyarar yini biyu a Afirka ta Kudu.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Ahmad Tijani Lawal