1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar karatun miliyoyin yara a Afirka

September 27, 2024

Yara da aka kiyasta sun kai miliyan biyu da dubu dari takwas na cikin hadari saboda rigingimu da tashe tashen hankula. Wannan hali ya fi kamari musamman a Najeriya da Kamaru.

Hoto: picture-alliance/AP Photo/UNICEF/Dicko

Tashe-tashen hankulan da ke ci gaba a fadin yammaci da tsakiyar Afirka sun kawo tsaiko ga karatun yara kusan miliyan uku a bisa alkaluman bayan bayan nan na rahoton Majalisar Dinkin Duniya. An rufe makarantu sama da 14,000 a yankin a zango na biyu na shekarar 2024 adadin da ya dara makarantun da aka rufe a bara da kimanin 1000.

A duniya baki daya yawan yaran da ba sa makaranta sun kai yara miliyan 250 a cewar alkaluman kungiyar raya Ilmi, kimiya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO. Nahiyar Afrika kudu da hamadar Sahara na da kashi 30 cikin dari na yaran da ba sa makaranta a duniya, alkaluman kuma na dada karuwa. Dauki ba dadi da makami ya kassara al'umomi ya kuma tagaiyara mutane da yawa kamar yadda Dr Ibrahim Baba Shatambaya, masanin kimiyar siyasa a jam'iar Usman Danfodio Sokoto a Najeriya ya shaida wa DW.

"A yankunan da tashin hankali ya tagaiyara al'umomi, sun yi kaura zuwa yankunan da ba nasu ba a matsayin mutanen da rikici ya raba da muhallansu, kuma za ka ga babban kalubalen da suke fuskanta ba wai ilmi ba ne, a'a amma samun muhimman bukatun rayuwa kamar abinci da ruwa da kuma harkokin lafiya."

Hoto: Imago/F. Stark

Haka kuma akwai batun tashin hankalin da ke shafar makarantu kai tsaye. Kai wa makarantu hari da gangan da makarkashiyar hana yara samun ilmi saboda tashin hankali, wannan ba komai ba ne face bala'i a cewar Dr Ibrahim Shatambaya.

"A Najeriya musamman arewa maso yamma mai yiwuwa kana da labarin cewa yawan kai hare hare a makarantu da sace sacen mutane da sauran munanan laifuka sun sanya wannan yanki na kasar cikin rashin kwanciyar hankali".

Kasashe kamar Najeriya da Kamaru da Burkina Faso da Mali da kuma Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango suna shan ukubar wannan tashin hankali yayin da kungiyoyin yan bindiga suke yawan kai wa makarantu hare hare.

Dalilan da suka haifar da tashe tashen hankula a wadannan yankuna suna da dama a cewar Dr Michael Ndimancho masanin kimiyyar siyasa a Jami'ar Doula a Kamaru.

"Idan ka kalli kasashe kamar Najeriya da Kamaru, Najeriya na fama da Boko Haram, duka wadannan batutuwa ne da suke da tarihi. Idan ka dubi Kamaru, ana fama da rikici a arewa maso yamma da kudu maso yamma, wadannan duk rikice rikice ne na mulkin mallaka.  Na yi imani akwai sa hannun wasu daga wage, ka gane daya daga ciki shi ne ma'adanan da aka gano a yammaci da tsakiyar Afirka, kuma hanya daya da wasu daga waje za su iya shigowa cikin sauki su kwashi wadannan albarkaru ita ce haddasa fitina."

Hoto: imagebroker/imago images


Yankin Kamaru da ke magana da turancin Ingilishi shi ma yana fuskantar irin wannan yanayi. A bisa alkaluman Majalisar Dinkin Duniya da na UNICEF a 2021 yara 700,000 ba sa zuwa makaranta, hakaa 2019 yara 855,000 ba sa zuwa makaranta a arewa maso yamma da kuma kudu maso yammacin Kamaru inda kungiyoyin yan aware suke kai hare hare a makarantu.

Illa mai tsawo da hana miliyoyin yara samun Ilmi zai haifar a nan gaba, tuni aka fara jin radadinsa a fadin nayiyar Afirka a cewar Dr Ndimancho. Kuma dukkan kokari na magance wannan matsala ta Ilmi a sassan duniya suna cin karo da juna kamar yadda kwararru suka nunar. Yayin da a waje guda kungiyoyin kasa da kasa kamar Majalisar Dinkin Duniya suka bayar da wasu tallafi, manazarta na ganin yunkurin bai wadatar ba yadda za a magance tushen matsalolin.