Makomar takarar Hama a zaben Nijar
January 12, 2016 Alhaji Mahamane Lawali da ke zama kakakin jam’iyyar Lumana Afrika da ta tsayar da Hama Amadou takarar shugabancin Nijar ya ce sun kudiri aniyar kalubalantar shugaba Mahamadou Issoufou a zaben watan Fabireru mai zuwa,
Wadannan kalaman masu zafi sun zo ne lokacin da sauran 'yan takarar shugabancin kasa cikin har da shugaba mai ci yanzu ke share fagen tinkarar yakin na neman zabe.
Sai dai ya ce ci gaba da garkame Hama Amadou a gidan kaso, bai zai hana jam'iyyarsa taka rawar gani a matakai daban-daban na zaben ba. Ya ce "in suna so, su ci gaba da rikeshi. Amma idan Allah ya yarda sai mun samu rinjaye cikin Nijar. Mun dauki matakan tashi mu yi wa jam’iyya aiki ko da irin wannan ta faru a gareshi."
Kotun tsarin mulkin Nijar ce ta tabbatar da takarar shugaban jam’iyyar Lumana duk da tuhumar da wata kotu take yi masa na marar hannu dumu-dumu a cikin badakalar safarar jarirai daga Najeriya: Sai dai wasu shika-shikkan 'yan adawar kasar suka ce ba a yi wa Hama Amadou adalci ba, ganin irin yadda daukacin takwarorinsa masu hannu a lamarin suka samu beli daga bangaren shari’a.
Mme Bayard Mariama Gamatche kakakin kawancen Adawa na FPR ta ce abin na bata mamaki, saboda " wadanda suka yi laifin tare da shi an sallamesu za su shiga yakin neman zabe. To don Allah ina bin ka’ida a cikin wannan lamarin? "
Babu dalilin ci gaba da tsare Hama Amadou
Ko da yake lawyoyin Hama Amadou ba su samu takamammai dalilan da suka kai ga kotu hana baiwa shugaban jam’iyyar ta Moden Fa sakin talala ba, amma su na da wa’adi na karin wasu kwanaki biyar domin tunkarar kotun kan bukatarsu ta bashi sakin na talala,
Malam Hama Amadou ya kasance a matsayi na uku a zaben shugabancin kasa na watan Janairun 2011 wanda hakan ta bashi damar mara wa shugaban kasa mai ci yanzu baya, bayan da ya balle daga wani kawancen na ARN. Abin da ya kai bangarororin biyu na PNDS-Tarayya da Moden-Lumana kafa gwamnati: Sai dai bayan shekaru biyu da rabi tafiyar ta waste tsakaninsu.