1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar Afirka ta fannin kasuwanci

July 5, 2019

Taron kolin da shugabannin Afirka za su gudanar karshen mako a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar zai mayar da hankali musamman kan yarjejeniyar ciniki maras shinge sai dai akwai wasu shirye-shiryen da aka gaza aiwatawa.

Mauritanien AU Gipfel
Hoto: Getty Images/A.O.M.O.Elhadj

Kudurori 14 da ke a cikin Ajenda ta 2063 za su share wa Afirka hanyar samun kyakkyawar makoma. Taron kolin da shugabannin kasashen Afirka za su gudanar karshen mako a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar zai mayar da hankali musamman kan yarjejeniyar ciniki maras shinge, sai dai har yanzu akwai wasu shirye-shiryen da aka kasa aiwatar da su.

Hoto: picture-alliance/ZUMAPRESS/G. Dusabe

Kamata nahiyar Afirka ta samu bunkasa ta bai daya, wannan dai shi ne burin kungiyar tarayyar Afirka AU da a karshen wannan mako ke gudanar da taron koli a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar. Jigo a jadawalin taron shi ne Ajenda ta 2063 da ke zama gagarumin shiri da ke da nufin gaggauta ci-gaba da bunkasa a nahiyar. Ajendar ta kunshi kudurori guda 14 a fannonin ginshikan tattalin arziki, ilimi, kimiyya da fasaha, al'adu da kuma tabbatar da zaman lafiya. Sai dai kawo yanzu abubuwa ba sa tafiya kamar yadda ake fata.

Ga misali kuduri na biyar da ya tanadi wanzar da zaman lafiya a Afirka baki daya kafin shekarar 2020 har yanzu babu wani ci-gaba da aka gani kamar yadda Dessu Meressa na cibiyar nazarin harkokin tsaro da ke birnin Addis Ababa na kasar Habasa ya nunar.

Shi ma masanin kimiyyar siyasa daga kasar Togo Désiré Assogbavi ya fada wa tashar DW cewa tsagaita wuta da tabbatar tsaro na zama ginshikin samun ci-gaba, saboda haka idan ana fama da rikici a mafi akasarin yankuna na nahiyar Afirka zai wahala a aiwatar da kudurori Ajendar ta 2063.

Hoto: Getty Images/AFP/STR

Tambaya a nan ita ce shin Tarayyar Afirka na samun ci-gaba a shirye-shiryenta? Ga misali yarjejeniyar ciniki maras shinge da ke da burin karfafa harkokin ciniki tsakanin kasashen Afirka da sanya matsayin tattalin arzikin nahiyar a kasuwannin duniya. A ranar 30 ga watan Mayun 2019 yarjejeniyar ta fara aiki a kasashe 24 da suka rattaba mata hannu. Sai dai bisa ga dukkan alamu yarjejeniyar a kan takarda ta kai wato ba a fara aiwatar da ita ba. Désiré Assogbavi masanin kimiyyar siyasa daga kasar Togo Désiré Assogbavi da ke da ra'ayin cewa yarjejeniyar za ta canja makomar nahiyar.

Bisa ga dukkan alamu yarjejeniyar za ta samu tagomashi a tarin na karshen mako domin bayan jan kafa na tsawon lokaci tarayyar Najeriya da ta fi karfin arziki a Afirka ta ba da sanarwar za ta shiga cikin yarjejeniyar ta sakarwa harkokin kasauwanci mara.

Sai dai ganin yadda a baya aka gabatar da manya-manyan shirye-shirye amma wajen aiwatar da su aka samu tafiyar hawainiya, masana na masu nuna shakku cewa a wannan karon ma da wuya a samu biyan bukata. Sai dai sun yi fatan cewa bisa yadda wasu nahiyoyin suka samu nasara a Afirka ma nasarar ka iya samuwa matukar aka samu shugabanci na gari.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani