Makomar zabe da 'yan daba a Najeriya
March 28, 2019Talla
Kungiyoyin musamman sun nuna takaici yadda aka gudanar da zabe a wasu yankuna na jihohi biyar na Najeriya inda aka maimaita zaben gwamna da ba a kammala ba.
Kungiyoyin sun yi Allah wadai da amfani da ‘yan daba wadanda suka rika cin zarafin masu zabe tare firgita wanda suka ce hakan karan tsaye ne ga tafarkin dimukuraddiya a Najeriya.
Musamman matsalar tafi tazara a jihar Kano da wani sashe na jihohin Sokoto da Benue da kuma Bauchi. Matasa ne dai aka yi amafani da su a wannan abin takaici da aka kira da sunan zabe, a cewar Farfesa Jibo Ibrahim na cibiyar nazarin dimukurdiyya da ke Abuja.