Libiya: Ana taro kan rikicin kasar
January 23, 2020Bayan wani Kudiri mai karfi da ya fito daga taron Berlin na kasar Jamus don sulhunta rikicin Libiya, a wannan Alhamis, wakilai na wasu kasashe da ke makwabtaka da Libiya ke wani zaman taro a Aljiyas babban birnin kasar Aljeriya don tattauna mafita kan rikicin da ke kokarin durkusar da kasar ta Libiya.
Taro ne na son ganin an cimma matsaya na dindin a tsakanin bangaren gwamnatin rikon kwaryar Libiyan da Janar Haftar da ke fada da juna, baya ga haka ministan harkokin cikin gidan Jamus Heiko Maas ya kasance daga cikin wadanda za su hallaci taron na wannan Alhamis, Mista Maas ya ce akwai bukatar a kara azama a kuma hada karfi da karfe in har ana son ganin bayan rikicin.
kasashen da suka shirya wannan zaman tattaunawar, sun hada da Masar da Aljeriya da Tunisiya da Chadi da Sudan da kuma Mali. Libiya dai ta stunduma cikin rikici, bayan kisan shugaban kasar Mammar Ghadafi shekaru tara da suka gabata.