1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Malala Yousafzai na ziyara a mahaifarta

Binta Aliyu Zurmi
January 12, 2025

Fitacciyar 'yar fafutukar kare hakkin mata da kananan yara Malala Yousafzai ta isa mahaifarta domin jagorantar gangamin fadakar da mata muhimmancin ilimi.

Pakistan Islamabad 2025 | Malala Yousafzai beim Gipfel zur Bildung von Mädchen in muslimischen Gemeinschaften
Hoto: AFP

Malala ta bar Pakistan a 2012, bayan mayakan Taliban sun bude mata wuta a lokacin da take kan ganiyarta ta fadakar da yara mata muhimmancin ilmi.

Malala wacce ta samu kyautar zaman lafiya ta Nobel na ziyara a Pakistan da ke makwabtaka da Afghanistan, kasa daya tilo da ta hana mata zuwa makaranta domin neman ilmi a fadin duniya. 

Malala ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa tana cike da murna da farin ciki na sake dawowa gida domin ganawa da mata kan batun ilmi.

karin Bayani:Hunkunci a kan 'yan Taliban waɗanda suka nemi kashe Malala Yousafzai