Malamai na cikin kunci a Borno
October 5, 2017A ranar biyar ga watan Oktoba na kowace shekara ce Majalisar Dinkin Duniya ke bukin malamai don yin nazari da duba halin da malaman ke ciki da nufin inganta rayuwarsu.Taken ranar bukin a bana shi ne "Martaba Malamai, Inganta matsayin rayuwa." Malaman makarantun na taka muhimmiyar rawa wajen koyar da ilimi da tarbiyar yara, sai dai a wannan sashe na duniya suna cikin masu fama da Kuncin rayuwa da barazana, Nigeriamusamman yadda aka samu kungiyar da ke yaki da karatun boko a Najeriya. A cewar wani jami'i a kungiyar malamai ta kasa reshen jihar Borno, malamai na cikin mawuyacin hali tamkar 'yan fansho.
" Sama da shekaru biyar malaman firamare ba sa samun kudaden hutu ko karin girma ko dadin albashi, muna karbar albashi tsawon wannan lokaci ba karin ko kwabo."
Sai dai kwamishinan Ilimi a jihar Borno Hon. Musa Inuwa Kubo ya ce akwai rashin fahimta a wannan yanayin. Matsalar rashin inganta rayuwar malami na haifar da koma baya a kokarin bunkasa ilimi musamman a yankin da ake fama da kungiya mai yaki da karatun boko.
Wata matsala kuma ita ce malamai da dama ala tilas sun yi watsi da aikin karantarwa, wasu kuma su ka rasa nituswar da ake bukata domin koyarwa saboda matsalar tsaro, abinda ake ganin ya shafi koyarwar da ake yiwa dalibai.
To sai dai a cewar malama Hauwa Ibrahim Jauro da ke koyarwa a makarantar sakandare da ke Damaturu fadar gwamnatin jihar Yobe,ta ce an samu saukin matsalar karatu kuma ya fara inganta. To sai dai duk da haka a wasu jihohin, gwamnatoci na daukar matakai na kyautata jin dadin malmai kamar yadda shugaban kungiyar malamai ta kasa reshen jihar Gombe Usman Dauda Kwadan ya shedawa DW.
Shima kwamishinan watsa labarai na jihar Hon Umar Nafada ya tabbatar wa malaman jihar cewa gwamnati za ta dauki matakan kyautata rayuwar malamai.
Yanzu haka kuma matsin tattalin arzikin kasa da ake fama da shi a Najeriya, ya kara jefa yawancin malami cikin mawuyacin hali saboda albashinsu baya isa inda wasu wuraren ma ake fito na fito kafin malaman su samu albashin.