Malaman addini sun gana da sojin Nijar
August 13, 2023Talla
Ziyarar neman sulhu karkashin jagorancin Sheikh Bala Lau shugaban kungiyar Izallah ta Najeriya, ta gana da shugaban kasar Abdourahamane Tchani kuma sun bayyana masa da amincewar shugaban Najeriya suke tafe.
A karon farko tun bayan jyuin mulkin, sabuwar gwamnatin soji ta Nijar din ta amince da hawa tebirin tattaunawa da kungiyar Ecowas domin warware rikicin siyasar kasar ta hanyar lumana.
Sabon Firaiministan Nijar Lamine Zeine ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan zama na sama da sa'o'i uku da suka yi.
A daya hannun kuwa hambararen shugaban Nijar Mohammed Bazouum ya sami ganawa da likitansa a jiya, wanda ya tabbatar yana cikin koshin lafiya. Sai dai duk da bukatar malaman Najeriya na neman su gana da shi lamarin ya ta ci tura.