Jamus: Malaria ta halaka ma'aikatan jirgin sama
August 28, 2026
Cibiyar ta Robert Koch ta ce, ana zargin sauron da aka hakikance an dauko shi a jirgin ne sanadin kamuwarsu da cutar ta malaria. Ta kara da cewa, yanzu sauran mutane hudu na karbar magani a asibiti. A cewar Cibiyar ta Robert Koch da ke kula da yaduwar cututtuka a Jamus, rabon da a samu kamuwa da malaria daga filin jirgin saman tun 2023.
Abin da cibiyar ta ce, ya yi sanadiyyar samun kulawar gaggawa saboda ba kasafai ake samun cutar malaria a Jamus ba. Tun da fari dai hukumomin kula da filin jirgin sama na Frankfurt na Jamus din, sun sanar da rasuwar ma'aikaci daya da kuma wasu shida da suka kamu da malaria. Malaria dai ba bakon abu ba ce a Kudu da Saharara Afirka, inda dubban mutane ke rasa rayukansu sakamakon cutar duk shekara a kasashen yankin.