Malawi: An kama mataimakin shuaban kasa
November 25, 2022![Shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera](https://static.dw.com/image/60542492_800.webp)
Talla
Hukumar yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Malawi (ACB). ta cce Saulos Chilima ya karbi dalla dubu 280,000 daga Zuneth Sattar dan Birtaniya mai asilin Malawi don samun kwangilar gwamnati. Hukumar ta ce 'yan sanda da sojoji sun bai wa wasu kamfanoni biyar na Mista Sattar kwangiloli 16 na dala miliyan 150, tsakanin shekarar ta 2017 zuwa 2021. Shugaba Lazarus Chakwera, wanda aka zaba bisa alkawarin yaki da cin hanci da karbar rashawa, ya tube mataimakinsa daga mulki a watan Yuni da ya gabata. Tuni dai aka kame wasu ministoci da tsaffin ministoci dangane da lamarin da ake zargin mutane da dama na da hannu a ciki