1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Imani da maita ya yi zurfi a kasar Malawi

Abdul-raheem Hassan SB)(ZMB
January 18, 2022

Wata doka da ta samo asali tun lokacin mulkin mallaka na Burtaniya, ta saba wa wannan akidu da ke ci gaba da janyo cikas kan harkoki da dama.

Kenia Unterkunft für der Hexerei beschuldigte
Hoto: DW

Hukumar shari'a ta Malawi, ta sake bitar dokokin da ake da su game da maita kuma ta gano muhimmancinsu. Mai shari'a Robert Chinangwa, shi ne shugaban hukumar shari'a a Malawi ya kuma yi wa DW karin bayani kan matakin da suka sa gaba, na fara ambaton dokar maita na yanzu wadda aka samar a shekarar 1911. A loakcin dokar ba ta gano  wanzuwar maita ba, amma bincike ya gano yawancin Malawi a cikin kasar sun yarda cewa akwai maita. Ba camfi ba ne kawai, gaskiya ce, akwai maita kuma ana yin bokanci.

Hukumar tana ba da shawarar manyan gyare-gyare guda biyu ga dokar maita a Malawi. Suna ganin ya dace doka ta fara gane cewa akwai maita, na biyu kuma, maita ya zama laifi. Hakan na nufin ana iya gurfanar da mutanen da ake zargi da maita a gaban kotu, kamar yadda mai shari'a Robert Chinangwa ya jaddada.

Yanzu haka dai fusatattun mutane sukan kai hari har ma suna kashe mayu. A cewar Cibiyar Kare Hakkokin Dan Adam da Gyaran Halittu ta Malawi, hakan ya faru fiye da mako guda a cikin 2021 kadai. Fatan shi ne cewa wannan shari'a na iya hana daukar doka a hannu. Ministan shari'a na Malawi, Titus Mvalo, yana ganin sabuwar dokar za ta taimaka wajen tabbatar da adalci ga bangarorin biyu - dakatar da kashe-kashen jama'a da kuma hana mayu da matsafa daga cutar da mutane.

Zargin maita sau da yawa yakan kai ga waɗanda ba su da ikon kare kansu: tsofaffi, yara da marasa lafiya ko naƙasassu. Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun damu da cewa matakin bai fito karara ba yadda ya kamata mutane su kare kansu daga zargin maita ba, ko da yake a yanzu an gabatar da dokar bokaye da aka duba ga ma’aikatar shari’a domin ta gabatar wa majalisar dokoki don zama doka.