1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Malawi: Matharika na kan gaba a sakamakon zabe shugaban kasa

September 21, 2025

Sakamakon farko-farko na zaben shugaban kasar Malawi ya nuna cewa, tsohon shugaban kasar Peter Matharika na kan gaba a zaben da ya gudana a wannan makon.

Yaki neman zaben kasar Malawi na shekarar 2025
Yaki neman zaben kasar Malawi na shekarar 2025 Hoto: Amos Gumulira/AFP/Getty Images

Tsohon shugaban kasar Malawi, Peter Matharika na gaba da abokin takararsa, shugaba mai ci, Lazarus Chakwera a sakamakon farko-farko na zaben kasar da aka gudanar a wannan makon. Kuru'un mazabu biyar daga cikin 36 da hukumar zaben kasar ta kidaya sun nuna cewa, Matharika na da kashi 51 cikin 100 yayin da Chakwera ke da kaso 39. 

Karin bayani: Yau ake zaben shugaban kasa a Malawi

Dama masu sharhi sun yi hasashen cewa zaben zai fi yin zafi ne tsakanin'yan takarar biyu da suke cikin manyan jam'iyun Malawi. Magoya bayan Matharika mai shekaru 85, da ya mulki kasar daga shekarar 2014 zuwa 2020 na da yakinin cewa zai samar da hanyoyi masu inganci da kuma magance tsadar rayuwa da kasar ke fuskanta a yanzu, sai dai masu sukar lamirinsa sun zarge shi da nuna bangaranci, zargin da ya musanta. Hukumar zaben kasar ta gargadi 'yan takarar da ikrarin lashe zabe gabanin ta fitar da cikakken sakamakon zuwa nan da ranar 24 ga watan Satumbar nan ta 2025.