Malesiya: Mahathis zai zama Firaminista
May 10, 2018Firaministan Malesiya Najib Razak ya amince da shan kaye a zaben gama gari da aka gudanar a ranar Laraba. A wani jawabi da ya yi Najib Razak yace ya amince da zabin al’ummar Malesiya.
"Mun amince da zabin jama'a kuma jam'iyyar Barisan Nasional na kara jaddada kudirinta na martaba tafarkin dimokradiyya."
Najib ya kara da cewa sarkin Malesiya zai yanke hukunci akan wanda zai zama Firaminista na gaba kasancewar babu jam’iyyar da ta sami gagarumar rinjaye.
Kawancen jam’iyyun adawa karkashin jagorancin tsohon Firaministan kasar Mahathir Mohammed mai shekaru 92 sun sami mafi yawan kujeru a majalisar dokoki inda suka kayar da jam’iyyar Barisan Nasional wadda ta shafe kusan shekaru 60 ta na mulki tun bayan da kasar ta sami yancin kai.
Mahathir Mohammed yace yana sa ran za'a rantsar da shi Firaminista nan gaba a yau Alhamis.