1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: Abdoulaye Maiga ya zama sabon Firaminista

Abdullahi Tanko Bala
November 21, 2024

Gwamnatin mulkin sojin Mali ta nada Janar Abdoulaye Maiga a matsayin sabon Firaminista bayan korar Choguel Maiga kwana guda bayan da ya soki shugabannin gwamnatin sojin.

Screenshot - Colonel Abdoulaye Maiga I ECOWAS Rückzug von Mali, Burkina Faso und Niger
Hoto: Xinhua News Agency/picture alliance

Wata doka da shugaban gwamnatin mulkin sojin Colonel Assimi Goita ya fitar da aka sanar ta akwatunan talabijin din kasa ta tabbatar da nadin Manjo Janar Abullahi Maiga a matsayin sabon firaminista.

Kafin nadin nasa Abullahi Maiga shi ne kakakin gwamnatin Mali.

Nadinsa domin maye gurbin firaminista farar hulla ya nuna har yanzu sojoji su ke rike da ragamar mulki.

Shi dai tsohon firaministan da aka sauke Choguel Maiga ya fito fili a ranar Asabar da ta gabata ya soki gwamnatin kan rashin tsarin mayar da kasar kan mulkin dimokradiyya

Kasar ta yammacin Afirka ta fada rikicin 'yan Jihadi da na 'yan tawaye tun bayan juye juyen mulkin soji da aka samu a shekarar 2020 da kuma 2021.