1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ana zargin sojoji da laifin kashe daruruwan mutane

Ramatu Garba Baba
May 12, 2023

Majalisar Dinkin Duniya ta zargi sojojin Mali da na kasashen waje da laifin hannu a kisan fararen hula sama da 500 a yayin wani tashin hankali da ya auku a kauyen Moura.

Wasu sojojin Wagner a Mali
Wasu sojojin Wagner a MaliHoto: French Army/AP/picture alliance

Wani sabon rahoto ya ce, yawan mutanen da aka kashe a wani rikici a Mali a bara, ya kai dari biyar, rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya dora alhakin kisan kan dakarun kasar Mali da wasu sojoji na kasashen waje da suka je kauyen mai suna Moura da sun dakile wasu hare-hare daga mayakan jihadi. A can baya majalisar ta ce, mutum dari uku aka hallaka a kwanaki biyar da aka kwashe ana fada, kafin a wannan Jumma'ar ta fida wannan rahoton da a cikinsa ta ce, mutum kimanin dari biyar aka tabbatar sun mutu bayan zurfafa bincike.

Shedun gani da ido a kauyen na Moura sun ce, su gane sojoji fararen fata da suka yi ta harbi a lokacin, amma majalisar na zargin sojojin hayan Wagner na kasar Rasha da ke ikirarin taimaka wa Mali a murkushe mayakan jihadi da laifin hannu a kisan a yayin da Hukumar kare hakkin bil adama ta majalisar ta baiyana kaduwa da alakanta laifin da take hakkin dan adam.