An ceto yan kasashen yamma a arewacin Mali
March 14, 2020Talla
Rahotanni daga yankin Kidal na arewacin Mali sun tabbatar da gano wasu 'yan kasashen yamma biyu da aka yi garkuwa da su tun a shekarar 2018 a kasar Burkina Faso.
Rahotanni sun ruwaito rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya da ke Mali MINUSMA na cewa dakarun rundunar sun gano mutanen biyu, daya dan kasar Italiyar Luca Tacchetto da 'yar Kanada Edith Blais ne a kusa da yankin Kidal a wannan rana ta Asabar, kana kuma tun a shekarar 2018 ce suke hannun masu tayar da kayar baya da makamai, suka yi garkuwa da su a cikin kasar Burkina Faso.