1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: Faransa na murnar sakin jami'inta

August 14, 2026

Faransa ta ce ta yi matukar farin ciki da matakin da gwamnatin mulkin sojin Mali ta dauka na yi wa jami'in leken asirinta Yann Vezilier afuwa, bayan an yanke masa hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Hoto: Christian Liewig/ABACAPRESS/IMAGO

Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta tabbatar da sakin jami'in, wanda ya shafe kusan shekara guda a tsare a Mali.

Fadar shugaban Mali ta ce afuwar ba ta nufin an wanke Vezilier daga tuhumar da ake masa, tana mai umurtar shi da ya fice daga kasar nan take.

An kama Vezilier ne a ranar 13 ga Agustan 2025 tare da wasu jami'an sojin Mali, bisa zargin hannu a wani shiri na kitsa makarkashiya ga gwamnati.

Sakin nasa dai wani mataki ne da ba kasafai ake gani ba tsakanin Mali da Faransa, bayan shafe shekaru ana samun takun saka a dangantakar kasashen biyu.