Mali: Harin bam ya kashe mutane 47
January 18, 2017Talla
Harin kunar bakin wake da aka kai da wata mota ya yi sanadiyyar rayukan mutane 47 a sansanin soji a garin Gao da ke yankin arewacin kasar Mali.
Sanarwa da ta fito daga bakin mai magana da yawun sojin Mountaga Tall na nuni da cewar, daga cikin wadanda suka mutun har da 'yan kunar bakin waken guda biyar, a yayin da wasu mutanen 115 suka jikkata, 30 na cikin mawuyacin hali.
A cewar Abdedoula El Kader Toure na kungiyar sa kai ta Gao, wata mota ce makare da wasu abubuwan fashewa masu nasaba da bam, ta tarwatse a daidai lokacin da sojojin suke taro.
An yiwa motar fentin launin soji, wanda ya bata saukin shiga cikin sansanin ba tare da wata matsala ba.