1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rasha da Ukraine na baza koma a Afirka

Ehli David ATB/LMJ
August 7, 2024

Zargin kasancewar jami'an leken asirin Ukraine a Mali, na haifar da damuwa. To amma Rasha da Ukraine dukkaninsu sun tsunduma cikin Sudan dumu-dumu, wanda ya sa rikicin guda biyu ya zama mai sarkakiya.

Mali | Matsala | Tsaro | Abzinawa | Azwada | 'Yan Ta'adda | Wagner | Rasha | Ukraine
Akwai tarin sojojin hayar Rasha na Wagner a ksashen Afirka ciki har da MaliHoto: French Army/AP/picture alliance

A fakaice bayanin a bayyane yake cewa 'yan tawayen Abzinawa da masu taimaka musu sun sami galaba, kamar yadda wani hoto da 'yan tawayen na MNLA suka dauka a kusa da tutar Ukraine ya nuna. Manufar sakon dai shi ne a nuna cewa da 'yan Ukraine ne, aka kai harin kwantan bauna da ya hallaka sojojin hayar Rasha na Wagner da na Mali masu yawa. Wani jami'in leken asirin sojan Ukraine ma, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa makamancin wannan. A sakamakon haka sojojin da ke mulki a Malin, suka katse huldar diflomasiyya da Ukraine. A daya bangaren kuma lamarin na da sarkakiya, Ma'aikatar Harkokin Wajen Ukraine ta yi kira ga fadar mulkin Mali a Bamako da ta ba da hujjar da ta tabbatar da cewa akwai hannun Kyiv a harin da aka kai kafin daukar matakin katse huldar diflomasiya da ita. Wani kwararen masanin siyasar kasa da kasa Ulf Laessing ya ce, yana da shakku kan dalilan da kasar Malin ta bayar.

Mali na fama da matsalolin tsagerun Abzinawa da Azwad da ma ta 'yan Ta'adda Hoto: Souleymane Ag Anara/AFP/Getty Images

Dambarwar sojan hayar Rasha wadanda ya kamata su taimaka wajen inganta tsaro a yankin Sahel a madadin sojojin juyin mulki da kuma sarkakiyar kasancewar jami'an leken asirin Ukraine a Mali, ta sanya aza ayar tambaya kan manufar Rasha da Ukraine ta yakin sunkuru a Afirka. Sai dai masanin harkar tsaron Ukraine Iliya Kusa ya ce, bai yarda cewa kasarsa na da hannu a harin na arewacin Mali ba. Maimakon haka ya shaida wa tashar DW cewa, kafofin yada labaran Rasha sune suka kambama labarin. Ita ma a nata bangaren wata malamar tarihin Rasha da ke Jami'ar Cape Town a Afirka ta kudu Farfesa Irina Filatova ta ce ba za ta iya yanke hukunci ba, sai dai bisa bayanai da ake samu Ukraine na da wani muradi da take son ta cimma. Gaskiyar lamari a yakin Sudan da ke ci gaba kusan shekara daya da wata hudu bayan barkewar yakin, yana da nasaba da yadda ake tura makamai daga manyan kasashen yankin kamar Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Masar. Sai dai kamar yadda wani manazarci a Kyiv ya ke cewa ko kadan Ukraine ba ta da wata sha'awa ko buri a Sudan, tana da muradi ne dai kawai a duk inda Rasha ta sa kafa.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani