1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan halin da ake ciki a Mali

Gazali Abdou Tasawa LMJ
May 25, 2021

'Yan kasar Mali mazauna Jamhuriyar Nijar da ma wasu masu fafutukar kare hakkin dan Adam, sun soma tofa albarkacin bakinsu kan halin da aka shiga a kasar Mali.

Mali | Interimspräsident Bah Ndaw
Shugaban gwamnatin rikon kwaryar Mali Bah Ndaw ya shiga komar sojojin kasarHoto: Amadou Keita/Reuters

A yanzu haka dai sojojin na tsare da shugaban kasar na rikon kwarya Bah Ndaw da firamnistansa Moctar Ouane a babban barikin soja na Kati da ke Bamako babban birnin kasar ta Mali. Matakin sojojin dai na zuwa ne, sa'o'i kalilan bayan da shugaban gwamnatin rikon kwaryar Bah Ndaw ya yi garan bawul ga gwamnatinsa, inda ya cire wasu manyan sojoji biyu wadanda ke rike da mukamin ministan tsaron kasa da na tsaron cikin gida daga mukaminsu, tare da maye gurbinsu da wasu janarorin soja biyu.

Karin Bayani: ECOWAS ko CEDEAO ta cire takunkumi a Mali

Rahotanni sun nunar da cewa wasu sojoji daga babban barikin soja na Kati ne suka zo suka tisa keyar shugaban kasar da firamnistansa zuwa barikin sojan, tare da tsare su. Maiga Issoufou Maiga shi ne wakilin jam'iyyar adawa ta SADI ta kasar Mali a Nijarz, kuma ya danganta sake bullar matsalar da sabanin da ake samu tsakanin masu goyon bayan Rasha da masu goyon bayan Faransa a tsakanin manyan sojojin kasar da kuma katsalandan din kungiyar ECOWAS a rikicin na Mali.Dubunnan 'yan kasar Mali ne dai ke rayuwa shekaru da dama a birnin Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar Nijar, kuma da dama sun nuna damuwarsu da halin da kasar tasu ta shiga.

Firaministan gwamnatin rikon kwaryar Mali da ya shiga komar sojoji, Moctar OuaneHoto: Presse- und Kommunikationsdienst des Premierministers von Mali

Rikicin da Mali ta shiga shekaru da dama dai, na matukar yin tasiri ga matsalolin tsaro da Nijar take fuskanta a yanzu. Wannan ne ma ya sanya Malam Lawal Sallaou Tsayyabou wani mai fafutukar kare dimukuradiyya a Afirka, ya yi kira ga shugabannin nahiyar da su gaggauta daukar mataki a kan wannan lamari na kasar Mali ta hanyar taka birki ga sojojin.

Karin Bayani: Za a kafa gwamnatin rikon kwarya a Mali

Duk da yake cewa sojojin Malin suna ci gaba da tsare shugaban kasar da firamnistansa, har kawo yanzu ba su fito sun yi wa duniya bayani kan manufarsu ba. Sai dai wasu majiyoyin na cewa sojojin sun yi juyin mulki ne kawai, amma a halin yanzu suna neman tilasta wa shugabannin gwamnatin rikon kwaryar su amince su yi murabus daga mukamansu. Sai dai tuni a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fiatar, manyan kasashen duniya kamar Amirka Jamus da Faransa da kungiyoyin EU da AU da ECOWAS, sun yi tir da abin da suka kira juyin mulki.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani