1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

COVID-19: Mali ta bar Masallatai a bude

April 30, 2020

Al'umma na bayyana mabambantan ra'ayoyi dangane da matakin da gwamnatin kasar Mali ta dauka na na barin Masallatai a bude a cikin wannan yanayi na annobar Coronavirus da ta addabi duniya.

Gabun Moschee
A kasashe da dama an rufe wuraren ibada, sai dai a Mali ba a rufe baHoto: Imago Images/robertharding/M. Runkel

Duk da dokar ta baci da ma ta hana yawon dare da ta dauka a yunkurin hana yaduwar annobar Coronavirus a kasar, Malin wacce kaso 95 daga cikin 100 na al'ummarta Musulmi ne, ba ta bayar da umurnin rufe wuraren ibada ba, sai dai ta bai wa limaman Masallatan kasar zabin budewa ko rufewa. 

Fargabar yada COVID-19

To sai dai tun bayan soma azumin watan Ramadana da Musulmi suka soma yin cincirindo a Masallatan, wasu 'yan kasar suka fara nuna fargabar ka da Masallatan su zamo tungar yaduwar annobar. Wannan fargabar dai ta sanya al'ummar kasar da dama fara amfani da kafafen sada zumunta na zamani, wajen yin kira ga gwamnati ta dauki matakin rufe Masallatan, musamman ta la'akari da yadda cutar ke kara yaduwa a kasar. 

Imam Mahmoud DickoHoto: Getty Images/AFP/H. Kouyate

Babban limamin nan na kasar mai farin jini da kuma karfin fada a ji, wato Mahmoud Dicko ya taka muhimmiyar rawa wajen hana gwamnatin Malin daukar matakin rufe Masallatan, inda ya kalubalanci mahukunta da cewa babu dalilin da zai sa bayan ta amince da shirya zabuka a kasar a tsakiyar annobar, a wayi gari kuma ta ce wa limamai su rufe Masallatansu domin hana yaduwar annobar. Baba Dakono na cibiyar bincike kan harakokin tsaro ta ISS da ke Bamako babban birnin kasar ta Mali, na ganin gwamnatin na kauce wa haifar da wani rikici ne a kasar da ta kwashe shekaru da dama matsalolin zamantakewa da na tsaro.

Tasirin malaman addini
Abdoulaye Guindo dan jarida kana shugaban shafin Internet na Benbere a kasar ta Mali, na ganin tasirin da shugabannin addini ke da shi a kasar ne ya hana gwamnati daukar matakin rufe Masallatan. Zuwa yanzu dai, annobar ta kashe mutane 25 daga cikin 482 da suka kamu da Coronavirus din a kasar ta Mali. 

Mali na fama da CoronaHoto: AFP/M. Cattani

Sai dai duk da haka ta la'akari da yadda annobar cutar ta Covid 19 ke kara yaduwa a kasar, wasu limaman sun dauki matakin rufe masallatan nasu har ya zuwa lokacin da kurar annobar za ta lufa. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kotun kolin kasar Jamus ta bayar da umurnin sake bude wuraren ibada da aka rufe sakamakon annobar, tana mai cewa matakin rufe wuraren ibadar ya saba wa 'yancin gudanar da addini wanda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar. Tuni dai matakin kotun ya soma haifar da muhawara a Jamus din, ta la'akari da yadda sannu a hankali annobar ke kara kamari a kasar, inda kawo yanzu ta kashe mutune kusan 6,500 cikin mutane 162 da suka kamu.