Mali: Masu shirin kai hari a Bamako sun shiga hannu
January 28, 2017Talla
Harin dai an tsara kai shi ne tun yayin babban zaman taron kasar Faransa da kasashen Afirka da ya gudana a ranaikun 13 da 14 ga watan nan na Janairu, amma kuma ta sabili da kwararan matakan tsaron da aka dauka a wurin taron hakan ba ta samu ba. Shi ya sa masu ikirarin Jihadin suka dage wannan danyan aiki na su har ya zuwa wani lokaci. Mutanen biyu dai da aka kama 'yan kasar ta Mali ne da aka haifa a yankin arewacin kasar, inda daya mai shekaru 29 an haife shi ne a birnin Gao, yayin da dayan kuma mai shekaru 21 a garin Intillit.