Matakin warware rikicin tawayen Mali
June 20, 2015 Bayan rikici mai nasaba da banbancin ƙabila, lokaci ne kuma da ake cike da fargabar ayyukan masu iƙirarin Jihadi.Wannan yarjejeniya ta Aljeriya na da burin ganin an samu haɗin kai tsakanin ɓangarorin 'yan tawayen da ayyukansu ke ƙara dagula lamuran wannan ƙasa ta Mali tun a shekarun 1960 sannan ga kutsen mayaƙan Islama masu alaƙa da Ƙungiyar Al-Ka'ida a arewacin ƙasar mai yawaitar Sahara.
Tun a watan Mayu, aka rattaɓa hannu tsakanin ɓangaren gwamnati da 'yan tawaye da suka miƙa wuya, sai dai ɓangaren ƙawancen Azawad ya ɓalle daga cikin yarjejeniyar, sai a makwanni biyu da suka gabata bayan sake kwaskwarima ga shirin zaman lafiyar.
Ministan harkokin wajen Holland kuma tsohon jagoran shirin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya a Mali Bert Koenders tare da takwaransa na Faransa Laurent Fabius sun yi lale marhabun da shigar ƙawancen na Azawad, dan haka sai suka buƙaci ɓangaren gwamnatin ta Mali ya maida hankali wajen ganin an aiwatar da yarjejeniyar.