1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin kabilanci da ta'addanci a Mali

Abdoulaye Mamane Amadou LMJ
December 7, 2021

Rigingimu na kara kazancewa a yankin Segou da ke kasar Mali, bayan da 'yan bindiga suka yi kaka gida a yankin mai fama da rikice-rikice na ta'addanci da kabilanci.

Mali Bankass | Ausgebrannter Bus nach Bewaffnetem Angriff
Rikicin kabilanci da matsalar tsaro na addabar kasar MaliHoto: ORTM/REUTERS

Wannan matsala dai na kara kawo cikas ga al'ummar yankin, musamman ma a fannin shige da fice tare diga ayar tambayar cewa ko kara dagulewar al'amuran yankin ka iya shafar babban birnin kasar ta Mali wato Bamako? Kusan kullum a kan ga mutane dauke da muggan makamai masu kama da juna bila adadin a garin Farabougou na yankin Segou, sau tari kuma a kan ga mutane na zagaye a cikin motocin soja kirar pick-up da babura har ma da motoci masu sulke, wanda hakan ke nuni karara cewar masu gwagwarmaya da makamai ne ke da karfin fada a ji a yankin.

Karin Bayani: Goodluck Jonathan zai sasanta rikicin Mali

Wasu alkaluma da Hukumar Kula da Ayyukan Jin Kai ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA ta fitar a tsakankanin watan Yuli zuwa Satumbar wannan shekarar ta 2021, sun bayyana cewa fiye da mutane dubu 24 ne suka kauracewa gidajensu kana dubu 12 daga ciki sun balle ne daga gundumar Niono ta yankin Segou dan tsira da rai sakamkon rikicin. A cewar wani mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Drissa Kanambaye ba tun yau ba, masu dauke da makamai ke cin karensu babu babbaka a yankin. Masu dauke da makaman dai kan shafe tsawon lokaci suna kafa irin dokokin da suka ga dama a yankin, kana suna kona rumbunan abinci da gonakin shinkafa har ma da injinan noma.

Matsalolin tsaro a fadan kabilanci na haddasa karancin abinci ga al'ummar MaliHoto: AFP/Getty Images/I. Sanogo

Wasu masana na ganin cewar matsalar da ke neman ta gagari kundila a yankunan tsakiyar Mali da kudanci, ka iya nausawa zuwa babban binrin kasar Bamako nan gaba idan har ba gwamnatita yi wa tubkar hanci ba, batun da kuma ya fara bijiro da fargabar da zukatan jama'a suke da ita a fili. Galibin al'ummar da ke birnin Bamakon Mali dai sun fito ne daga yankin kudanci da yammcin kasar, yankunan da yanzu haka mayakan jihadi da kungiyoyin sa kai ke cin karensu babu babbaka. A hannu guda kuma, tashe-tashen hankulan da ke faruwa a yammaci na kara fadada har zuwa kusa da iyakar kasar da Senegal.

Karin Bayani: Jamus ta tsawaita zaman sojojinta a Mali

Sai dai duk da hakan da akwai wasu yankunan da ake kokarin karewa daga matsalolin na tsaro daidai gwargwadon hali, a cewar  Moussa Ag Acharatoumane wani kusa a gwamnatin wucin gadi ta Mali. Matsalar tabarbarewar tsaro dai a Mali na ci gaba da ta'azzara harkokin yau da kullum a cewar kungiyoyin bayar da agaji, yayin da yankunan kasar da dama suka fada yanayi na karancin cimaka. Wannan lamarin dai ya tilastawa dubban mutane ci gaba da gujewa matsugunansu domin tisra da rai, wanda kungiyoyin bayar da agajin suka ce tun a watan Fabarairun 2019 zuwa yanzu adadin ke karuwa.